Dakta Larijani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi wajen rufe kasuwar baje kolin littattafa na kasa da kasa karo na 27 da aka rufe yau a Tehran inda ya ce mutanen da suke tunanin ta hanyar takunkumi za su kashe wa al’ummar Iran gwiwa, lalle sun yi kuskure.
A saboda haka shugaban majalisar shawarar Musuluncin ta Iran ya ja kunnen kasashen yammancin da cewa irin wadannan siyasa ta su babu abin da za ta haifar musu in ban da kara kyamarsu da al’ummar Iran za su yi.
A safiyar yau ne aka gudanar da bikin rufe kasuwar baje kolin littafan na Tehran da ta dauki kwanaki 10 tana ci. ABNA.